Zargin gurbata tarbiya a Kano
Kotu a Kano ta aike da wasu matasa hudu 'yan TikTok gidan gyaran hali bisa zargin yada rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta biyo bayan kararsu da Hukumar tace fina finai tayi
Wadanda ake tuhuma su ne Hafsa Hamisu (Zoom Zoom), Usman Majidadiɓ (Majidadi), Sumayya Muhammad (Summy Beby), da Usman Ibrahim (Maikalar Kudi), kuma duk sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi.
Hukumar tace fina finai ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El- Mustapha ta sha alwashin ci gaba da yaki da rashin da’a a kafafen sada zumunta domin kare tarbiyya da al’adun al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.
Comments
Post a Comment