Zargin fataucin qwaya

 Ina zamu saka kan mu a Kano? 


Sunan sa Suleman Dan Wawu Fagge yanzu haka yana hannun jami’an NDLEA wasu al’umma daga Fagge sun shaida min cewar an san irin kasuwancin da yake Amma an masa shiru saboda tsoron abin da kaje yazo.


Babban abin takaicin shine wannan fa mutum ne da ake ganin sa yana fantamawa da manyan motoci da sauran Kayan alatun rayuwa, kuma da yawan mutane sun san irin kasuwancin da yake.


A shekarar 2022 an kama Shi kan tuhumar fataucin kwayoyi, amma babu dadewa aka sake shi yanzu haka an kama shi da irin wannan harkallar daga gun Yansandan an mika shi gun NDLEA amma can ma Wata Majiya me tushe tace matukar ba manyan mutane daga yankin su sun rubutawa kotu korafi kan irin cakar da yayansu da yake ba to Akwai yuwuwar sakin sa ko bayar da belin sa cikin kankanin lokaci. Ina da tambayoyi da yawa kan wannan mutum, na farko ya aka yi ya samo Mota da official plate number ta Presidency? Wacce hanya yake bi yana kubucewa idan an kama shi? Da zan ganshi da na sami amsoshin Wadannan tambayoyi.

Mu sani cewar galiban matsalolin mu na Daba da ta’addanci tushen su shine tu’amalli da miyagun kwayoyi Dan haka ya zama wajibi mu hada kai mu tunkari wannan muguwar Matsala.


Allah yayi mana tsari.

Comments

Popular posts from this blog

Wasu wuraren jimai badai gado ba

'Yanbindiga sun sace mutum 117 da hallaka wasu tara a Jihar Kebbi

Hanyoyi da miji zai bi wajan gamsar da iyali